Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar rasha ya danganta batun dakatar da bada wutar lantarki ne saboda rashin biyan takudade na watan mayu, sai dai masana sun nuna cewa batun baya rasa nasaba da kokarin kasar na hadewa da kungiyar tsaro na Neto
Wannan sanarwar tazo ne kwana daya bayan da shugaban kasa Sauli Ninisto da kuma fira ministan a kasar Sanna Marin suka bayyana aniyar kasar na hadewar da kungiyar tsaro ta Nato ba da bata lokaci ba.
Kasar rasha ta yi gargadin cewa shigar kasar Finland cikin kungiyar tsaro ta Nato babbar barazana ce gareta , inda ministan harkokin tsaron kasar rasha ya matakin zai tilasatawa Mosko daukar mataken da suka dace da suka shafi dabarun soji don magance wannan abin da take gani a amatsayin barazana
Kasar rasha tana makwabtaka da kasashe 14 5 daga cikinsu mamabobi ne a kungiayr tsaro ta nato su ne Latvia, Estonia, Lithuania, Poland, da kuma Norway.
342/